David Cameron ya ziyarci Shugaba Obama

David Cameron da Barrack Obama
Image caption David Cameron da Barrack Obama

Firayi ministan Birtaniya, David Cameron, yayi shawarwari tare da shugaban Amirka, Barack Obama, a Washington, a karon farko tun bayan da ya zama Firayi minista watanni biyu da suka wuce.

Mista Obama ya ce, Amirka bata da wata babbar kawa kamar Birtaniya.

Shi kuwa Mista Cameron ya ce dangantaka tsakanin Amirka da Birtaniya na da mahimmanci matuka, wajen tabbatar da tsaro da kuma bunkasar tattalin arzikin duniya.

Sai dai har yanzu a Amirkan ana jin takaicin yadda aka saki Abdelbasset Al Megrahi, mutumen da aka samu da laifin kai harin jirgin saman Lockerbie.

Wasu 'yan majalisar dokokin Amirkan sun yi amunnar cewa, kamfanin man Birtaniya na BP ne yayi kamun kafa har aka sake shi.