An rantsar da kwamishinonin hukumar zabe ta Najeriya

Farfesa Attairu Jega, Shugaban Hukumar zabe ta Najeriya
Image caption Farfesa Attairu Jega, Shugaban Hukumar zabe ta Najeriya

An rantsar da kwamishinonin zabe a Najeriya, a shirye-shiryen da ake na gudanar da babban zabe a kasar.

Kwamishinonin zabe goma sha tara ne suka yi rantsuwar yau a Abuja, a gaban shugaban hukumar zabe mai zaman kanta -INEC, Parfesa Attahiru Jega.

Shugaban hukumar zaben yayi kira a garesu da su kasance masu gaskiya da adalci wajen gudanar da aikin da aka damka masu.

A lokacin da yake rantsuwar kama aikin,Shugaban hukumar ya ce sahihin zabe a kasar zai tabbata ne kawai idan aka samu shugabannin hukumar masu rikon amana da gaskiya.

Wannan dai wani muhimmin mataki ne a shugabancin hukumar, musamman ganin yadda lokacin zaben shekarar 2011 ke kara matsowa.

Matsalar magudin zabe dai wata babbar matsala ce ga sha'anin shugabanci a Najeriyar wani abun da ake dangantawa da koma-bayanta.