An kara wa'adin sabunta rajista a Nijar

Janar Salou Djibo
Image caption Janar Salou Djibo

A Jamhuriyar Niger, hukumar zaben kasar ta bayar da sanarwar karin lokaci akan aikin sabunta rajistar masu zabe.

Hukumar ta ce ta kara kwanaki ukku domin tabbatar da sauran jamaa a kasar sun samu damar sabunta rajistarsu, bayan da mahukuntan kasar suka yi sassauci akan ka'idojin da aka gicciya na sabunta rajistar.

A yanzu za a kammala aikin ranar Alhamis ne sabanin ranar talata kamar yadda aka shirya a baya.

Hakan ya biyo bayan gyaran fuskar da hukumomin mulkin sojin kasar suka yi ne akan dokokin sabunta kundin sunayen masu kada kuru'ar.

A yanzu haka dai saboda wannan gyara jamaa masu takardar haihuwa na iya amfani da ita domin yin rajistar ko kuma sabunta katinsu na zabe.

Tun dai lokacin da aka fara shirin sabunta rajistar ne, jamaa da dama suka yi ta kokawa akan rashin amincewa da takardar haihuwar wajen sabunta katin zaben.