Hukumar abinci ta duniya za ta ribanya taimakonta ga Nijar

Wani yaro mai fama da tamowa a Nijer
Image caption Wani yaro mai fama da tamowa a Nijer

Hukumar abinci ta duniya WFP ta ce za ta rubanya agajin da take baiwa jamhuriyyar Nijar, don ciyar da kusan mutane miliyan takwas da sukayi asarar amfanin gonansu da kuma dabbobi a sanadiyar fari.

Babbar daraktar hukumar, Josette Sheeran ta bayyana farin da cewa wata masifa ce dake cigaba da afkawa miliyoyin mutane.

Inda ta kara da cewa lokaci na neman kure musu na cimma mutanen da ke fuskantar matsalar yunwan.

Ms. Sheeran ta bukaci a taimakawa hukumar, tana mai cewa shirin hukumar da aka fadada na bukatar fiye da dala miliyan dari biyu.

Ta ce hukumar za ta fi maida hankali kan kananan yara, wadanda ke fuskantar hadarin karancin abinci mai gina jiki.