Makamashin Yuraniyom na da muhimmanci ga Nijar

Wajen hakar mai a Nijar
Image caption Daya daga cikin wuraren da jama'a ke hakar Yuraniyom a Nijar

Tun lokacin mulkin Turawa aka fara gano ma'adanin Uranium a Nijar, watau a shekarar 1957 a yankin Azelik dake Arewacin kasar, shakaru uku kafin Nijar ta samu yancin kai.

An fara hako Uranium a Nijar a karshen shekaru 1960, tare da fitar da shi zuwa wasu kasashen duniya, musamman Faransa.

Ma'adanin Uranium ya kasance babbar hanyar samun kudin shigar Nijar da kashi saba'in da biyu cikin dari, sai kuma albarkatun noma da kiwo.

Zinare na daga cikin albarkatun kasar da aka gaano a Nijar, inda a shekara ta 2004, shugaba Tandja ya bude wani kamfani mai suna Samira Hill wanda ya fara hako gwal din a jahar Tera, kuma kasashen Morocco da Canada sue ke rike da kashi tamanin daga ckikin dari na jarin kamfanin, sannan gwamnatin Nijar na da kashi ashirin cikin dari.

A watan Janairun shekara ta 2003, shugaban Amurka George W Bush, ya zargi Iraqi da sayen ma'adanin Uranium daga Nijar domin amfani da shi wajen kera makamashin nukiliya.

Amma a watan Maris na shekara ta 2003, sai hukumar da ke kula da makamshi ta duniya, IAEA ta ce takardun da ke nuna alakar Uranium tsakanin Iraqi da Nijar na bogi ne, kuma zargin ba shi da tushe.

Allah ya albarkaci Nijar da man fetur a yankin Agadem na Gabashin kasar, abin da ya sa kasar ta shiga wata yarjejeniya da wani kamfanin China, CNPC da zai hako rijiyoyin mai goma sha daya, kuma zai fara hakar man ne nan da shekara ta 2012. Kamfanin na China zai kuma gina matatar mai a jihar Zinder wadda za ta rika tace gangar danyan mai dubu ashirin a kowace rana.