Nigeria ta fara saida kayan abinci cikin rahusa

Shugaban Nigeria
Image caption Dr Goodluck Ebele Jonathan

Gwamnatin Nigeria ta kaddamar da wani shiri na sayar da hatsi a farashi mai rahusa ga jama'a a Abuja babban birnin kasar.

Kamar yadda ministan aikin noma na kasar, Sheikh Ahmed Abdullah, ya bayyana, gwamnatin Nigeria zata gudana da wannan shiri a sauran sassan kasar.

Gwamnatin dai tace tayi hakan ne da nufin ragewa al'ummar kasar wahalahlun da suke fuskanta sakamakon tsadar abinci.

A wani mataki na taimakawa kasashen dake makwabtaka da ita, Gwamnatin Nigeria ta ce zata taimakawa kasashen Chadi da Jamhuriyar Niger da kayan abinci domin magance matsalar yunwa da kasashen ke fama da ita.

Tun a kwanakin baya ne dai kungiyar ECOWAS ta bukaci kasashen dake cikin kungiyar da su tallafawa wadannan kasashe da kayan agaji.