Za a kaddamar da yakin neman zabe a Rwanda

Shugaban Rwanda,Paul Kagame
Image caption An fara gangamin share fagen zaben kasar Rwanda

A ranar Talata ne ake kaddamar da gangami don share fagen zaben shugaban kasar Rwanda,wanda da za a gudanar a watan gobe.

Ana saran shugaban kasar Paul Kagame zai lashe zaben,sai dai share fagen zaben ya fuskanci koma-baya sakamakon zargin kisa,da kuma tsare manyan 'yan adawa da ake yiwa shugaban kasar.

Gwamnatin Rwanda dai ta musanta zargin,sai dai batun na kawo shakku dangane da yadda ake kare hakkin 'dan adam a kasar.

Mutane uku ne dai ke yin takara don neman kawar da jam'iyar shugaba Paul Kagame,wato Rwandan Partiotic Front.

Wannan shi ne karon farko da wasu jam'iyun ke takarar kujerar shugaban kasar.