An yi hatsaniya tsakanin Yan shi'a da Yan sunni a Sakkwato

Yansandan Najeriya
Image caption Yansandan Najeriya

An tsaurara matakan tsaro a birnin Sakkwato, bayan wani fadan da ya barke da safiyar yau tsakanin 'yan Sunna da 'yan Shi'a, inda wasu suka jikkata.

Lamarin ya faru ne yayin da mabiya Shi'ar ke jerin gwano, na neman gwamnatin jahar ta sako wasu 'yan uwansu da take tsare dasu.

A shekara ta dubu biyu da bakwai ne hukumomin Sakkwaton suka rusa wurin ibadar 'yan Shiar a garin, tare da kama mutane akalla dari da ashirin.

Hakan ya biyo bayan bindige wani fitaccen malamin Sunna, Malam Umaru Dan mai shiya, da ake zargi da sukar manufofin 'yan Shi'a a garin.