Amurka ta sanyawa Korea ta Arewa sabon takunkumi

Hilary Clinton
Image caption Hilary Clinton

Amurka ta saka sabon takunkumi a kan Koriya ta Arewa a sakamakon takaddamar da aka fuskanta kan nutsar da wani jirgin ruwan yaki na Koriya ta Kudu.

Amurka dai ta dora alhakin wannan al'amari akan Koriya ta Arewa.

A wata ziyara da t kai zuwa Koriya ta Kudu, Sakatariyar harkokin wajen Amurkar, Hilary Clinton ba ta bayar da cikakken bayani ba game da takunkumin, illa ta na mai cewar za a kara takaita saida makamai da kuma kayan alatu ga Koriya ta arewar.

Mrs Hilary Clinton ta ce za a iya cire takunkumin idan Koriya ta Arewa ta sauya halayyarta ta yin gadara ga makwabtanta.

Nutsar da jirign ruwan yakin Korea ta Kudun a watan Maris din daya gabata shine ya janyo wani sabon yanayin zaman dar dar a tsakanin Arewa da Kudu.

Har yanzu Korea ta Arewa na cigaba da nanata cewa babu hannunta a ciki.

Karuwar rashin tabbacin dai kamar yanda masana da dama ke gani shine shirin da shugaban Korea ta Arewan Kim Jong na biyu ke yi domin sharewa magajinsa hanya.