Binkice ya bayyana illar sinadarin asbestos

Kwanukan rufin da aka yi da sinadarin asbestos
Image caption Sinadarin asbestos na illa ga jama'a

Wani binkice da BBC,da kuma wata kungiyar 'yan jaridu suka gudanar ya gano yadda ake kashe miliyoyin daloli don bunkasa sayar da sinadarin asbestos mai yiwa mutane illa .

Harwayau, binciken ya gano cewa ma'aikatun sinadarin asbestos na shigar da shi zuwa kasashe masu tasowa,wadanda akasari basu da wata doka da take kare mutane daga haduran da sinadarai ke jefa su a ciki.

Masu kare yadda ake amfani da wannan sinadari sun ce ana amfani da mai launin fari ne,wanda ba shi da illa.

Sun kara da cewa farin asbeston din bashi da illa kamar dan uwansa mai launin ruwan kasa,da kuma shudi,kamar yadda binkicen kimiya ya bayyana.

An hana yin amfani da wadannan launuka na asbestos a duk fadin duniya saboda yadda suke kawo,sankara,da kuma cututtukan da suka shafi numfashi.

'Sinadarin asbestons na da matukar lahani ga lafiya'

Sai dai masu kare hakkkin dan adam,da kuma masana kimiya na da ja kan ikirarin masu kare yadda ake amfani da sinadarin na asbstos,inda suka ce hukumar lafiya ta duniya ta yi suka kan yadda ake amfani da sinadarin mai launin fari,saboda yana haddasa sankarar huhu.

Ita ma Tarayyar Turai ta hana amfani da sinadarin asbestos mai launin fari,sai dai ana ci gaba da amfani da shi a kasashen Indiya,da Rasha,da kuma China.