Inshorar matafiya motocin haya a Najeriya

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Majalisar wakilan Najeriya ta yi zaman sauraron jin ra'ayoyin jama'a, a game da wani kudurin doka kan samar da inshora ga fasinjojin motocin haya a kasar.

Manufar kudurin dokar ita ce, a taimakawa wadanda hadari ya rutsa da su, ta hanyar biyan su diyya da kuma kudaden jinya.

Sai dai masu adawa da inshorar na ganin cewa, hakan zai iya sa wa kudin shiga mota ya karu, ganin cewa sai an biya kudin inshorar ne kafin mutum ya cancanci samun diyya, idan hadari ya rutsa da shi.