Shugaban babban bankin Najeriya ya koka

Shugaban babban bankin Najeriya,Sanusi Lamido Sanusi
Image caption Sanusi ya soki tsare-tsaren gwamnatin kasar kan inganta wutar lantaki

Shugaban babban bankin Najeriya,Sanusi Lamido Sanusi ya nuna damuwa a bisa tsare tsaren gwamnati na samar da wadatacciyar wutar lantarki ga jama'ar kasar.

Da yake jawabi a wani taro a Kaduna,Malam Sanusi ya jaddada cewa matsalolin tattalin arzikin kasar ba wai sun rataya ne kawai a wuyan bangaren gudanar da bankunan kasar ba.

Ya ce daya daga cikin abubuwan dake kassara tattalin arzikin kasar, shi ne rashin kyawawan manufofin samar da tsayayyiyar wutar lantarki, wacce keda muhimmanci wajen habbakar tattalin arzikin kasa.

Irin wadannan kalaman na shugaban babban bankin dai ba kasafai su kan fito daga bakunan manyan jami'an gwamnatin kasar ba.