Halin rayuwa a Jamhuriyar Nijar

Rayuwa a Nijar
Image caption Jama'a da dabbobi da dama na rayuwa ne cikin sahara a Nijar

Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a shekara ta 2008 ya nuna cewa kasar Norway ce kan gaba, yayinda Nijar ta zamo kurar baya a jerin kasashen duniya da rayuwa ta fi inganci.

An dai kasafa kasashen 182 ne ta hanyar yin la'akari da yadda mazauna kasashen ke rayuwa.

Kiyasin ya duba yadda tsawon rayuwar jama'a da matsayin ilimi da yadda yara ke samun damar halartar makaranta da kuma tattalin arzikin kasar.

An hada alkaluman wannan rahoto ne a shekara ta 2007-kafin a shiga matsalar tattalin arzikin da duniya ta yi fama da shi.

Hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya, UNDP ko PNUD ta ce alkaluman sun nuna yadda ake da banbance-banbance tsakanin masu hali da marasa shi.

Nijar ta samu kanta a wannan hali ne sakamakon matsalar farin da kasar ke fama da shi, abin da a wasu lokutan ya kan sa kasar ta kasa ciyar da jama'arta.

Kiyasin ya nuna cewa al'ummar Nijar za su iya rayuwa ne kawai ta tsawon shekaru 50-kusan banbancin shekaru 30 da takwarorin su na kasar Norway.

A kan kowacce dala daya da mutum guda ya samu a Nijar, a kan samu dala 85 ne a Norway.

Image caption Karancin abinci ya jefa yara da dama cikin wahala a Nijar

A zahiri take cewa jamhuriyar Nijar na fama da matsanancin talauci, musamman bayan da kasar ta yi fama da matsanancin fari, kasancewar mafiya yawan jama'ar ta manoma ne.

Irin wannan hali da kasar ta samu kanta a ciki a shekara ta 2005, ya jefa miliyoyin 'yan kasar cikin yunwa da rashin abinci mai gina jiki.

Har ila yau, kungiyar dada agaji ta Burtaniya Save the Children, ta yi gargadin cewa kimanin 'yan kasar miliyan takwas ne suke fama da barazanar yunwa sakamakon farin da ake fama da shi.

Shugaban kungiyar agaji ta Red Cross, ya bayyana yankin Diffa na Gabashin Nijer din , da cewa ya fi kowanne fuskantar barazana, inda akalla kashi tamanin cikin dari na jama'ar yankin ke bukatar taimakon abinci.

Tuni dai kasashen duniya da ma kungiyoyin agaji da dama suka fara kaiwa kasar agajin kayan abinci.

Mutumin da ya rubuta rahoton Jeni Klugman, ya ce: "kasashe da dama sun fuskanci matsala a 'yan shekarun da suka gabata, ta fuskar tattalin arziki da kuma matsalolin rikice-rikice.

Haka kuma matsalar tattalin arzikin da duniya ta yi fama da shi, ya sa kasashen da ke bada agaji, rage irin agajin da suke bayarwa.

Abin da kuma ya jefa kasashe matalauta irin su jamhuriyar Nijar, cikin halin kaka-ni-kayi.