Tarihin Jamhuriyar Nijar

Taswirar Nijar
Image caption Jamhuriyar Nijar ta samu 'yan cin kai ne daga turawan Faransa a watan Agusta na shekarar 1960

Jamhuriyar Nijar ta samo sunan ta ne daga kogin Naija duk kuwa da cewa ba ta kusa da wata babban mashigin ruwa. Nijar na makwabtaka da Najeriya da Benin ta kudanci, Burkina Faso da Mali ta yammaci, Aljeriya da Libiya ta arewaci, sai kasar Chadi ta bangaren gabas.

Kodayake sai a cikin karni na goma sha tara ne Turawa kamar Mungo Park dan kasar Burtaniya, suka fara shiga can bangaren kogin Naija, to amma dai tun kafin wannan lokacin Faransa ke ta kokarin ganin ta mallaki Nijar, inda ta samu nasara a shekarar 1890.

A wannan lokaci Faransa ta na da gwamnonin dake tafiyar da harkokin dukkanin yankunan da ta mamaye a yammacin Afirka ciki harda Nijar, wadanda ke aiki karkashin babban gwamna, wanda ke zaune a Dakar na kasar Senegal.

Ranar goma sha takwas ga watan Disambar shekarar 1958, Niger ta zamo Jumhuriya mai cin gashin kanta a karkashin ikon Faransa.

Sannan a ranar uku ga watan Agusta na 1960, jamhuriyar Nijar ta samu 'yancin kai, wato shekaru hamsin da suka wuce.

Image caption Dauda Malam Wanke ya shugabanci Nijar a shekarar 1999, bayan wani juyin mulkin soji

Kalubale

Jamhuriyar Nijar ta yi fama da juyin mulki daga sojoji daban daban wadanda suka mamaye madafen iko a kasar bayan ta samu 'yancin kai.

Kasar wacce ke fama da matsanancin fari, na fadi-tashin ciyar da jama'arta.

Babban abin da take fitarwa dai shi ne ma'adanin Uranium wanda shi ma a shekarun baya ya fuskanci rashin tabbacin farashi, yayin da kwararowar hamada ke barazana ga aikin noma.

Amma a gefe guda kasar na fatan fara hako man fetur wanda ka iya bunkasa tattalin arzikinta.

Bayan samun 'yancin kai, kasar ta fuskanci mummunan fari wanda ya lalata albarkatun noma.

Kasar dai ba ta da wani tsarin ilimin Firamare na azo a gani, abin da ya sa take cikin jerin kasashen da ke fama da rashin ingantaccen ilimi a duniya.

Harkar lafiya ma ba ta da kyau sosai, kuma akwai yaduwar cututtuka a ko'ina cikin kasar.

A lokuta da dama kasar ta yi fama da boren 'yan tawayen Abzinawa a Arewacin kasar.

Sai dai a shekara ta 2009, gwamnati da 'yan tawayen sun sanya hannu kan yarjejeniyar samar da zaman lafiya a birnin Tripoli na kasar Libya.

Shugaban mulkin soji: Salou Djibo

An bayyana babban jami'in soji Salou Djibo, a matsayin shugaban gwamnatin sojin kasar, bayan da sojoji suka hambaras da gwamnatin shugaba Mamadou Tandja a watan Fabrairun shekara ta 2010.

Jami'an sojin sun yi alkawarin mayar da kasar kan tafarkin dimokradiyya, sannan suka nada Fira minista farars hula Dr Mahamadou Danda, a matsayin shugaban gwamnati.

Hukumomin sun kuma haramtawa kansu da kuma jami'an gwamnatin rikon kwariya, shiga harkokin zaben kasar.

Image caption Manjo Janar Saliou Djibou ya hau mulki sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Fabrerun shekara ta 2010

Juyin mulkin ya sa Tarayyar Afrika ta dakatar da kasar daga kungiyar, sai dai kasashen duniya sun yi taka tsantsan wajen Allah wadai da matakin da sojojin suka dauka, inda suka neme su da su maida kasar kan tafarkin dimokradiyya.

An haifi shugaba Janar Salou Djibo a shekarar 1965 a Arewacin yankin Tillaberi.

Ya samu horon soji a kasashen Ivory Cost da China da Morocco, sannan ya yi aiki da tawagar sojin kasar da ta yi aikin kiyaye zaman lafiya karkashin Majalisar Dinkin Duniya a kasashen Ivory Cost da jamhuriyar Congo.

Kafafen yada labarai

Gwamnati ce ke da mallakin kusan baki dayan kafafen yada labaran kasar, sai dai a 'yan shekarun nan an samu karuwar kafafen yada labarai masu zaman kansu.

Kafar Rediyo ita ce hanya mafi sauki da girma ta samun labarai a Nijar, akwai kuma jaridu na gwamnati da masu zaman kansu.

Gidan Radiyon Faransa na watsa shirinsa ta tashar FM a biranen Yamai da Maradi da kuma Zindar. Haka kuma ana kama BBC a zangon FM a gidajen rediyo masu zaman kansu da dama.

Akwai kuma masu amfani da hanyar sadarwa ta Intanet kimanin dubu tamanin a watan Yuni na shekara ta 2009.