Sassa da yankunan jamhuriyar Nijar

Yankunan Jamhuriyar Nijar
Image caption Wani bangare na sahara a yankin jihar Maradi ta Nijar

Gabanin samun 'yancin kan Nijar an kasa kasar Nijar cikin yankunan mulki goma sha shida wadanda suka hada da Agadez, Birni N'Konni, Dogondoutchi, Dosso, Filingue, Goure, Madaoua, Magaria, Maradi, N'Guigmi, Niamey, Tahoua, Tera, Tessaoua, Tillaberi da Zinder.

Bayan da Nijar ta samu 'yancin kai a shekarar 1960, an kafa wata dokar tsara yankuna wadda a watan Disambar 1961, ta kirkiro da wasu yankuna 31. A wannan lokacin yankunan mulki 16 da ake da su sun ci gaba da kasancewa.

A watan Agustan 1964, dokar tsara yankunan ta sake kasafta Nijar zuwa yankuna bakwai, wadanda suka hada da Agadez, Diffa, Dosso, Maradi, Tawa, Tillabery da kuma Zinder. Sai kuma Yamai a matsayin babban birnin kasar.

An rarraba wadannan yankuna bakwai zuwa gundumomi talatin da shida wadanda su kuma aka sake rarraba su zuwa kananan kauyuka daban daban. A shekara ta 2006, Niger na da kananan kauyuka da magadan gari ke shugabanta har dari biyu da sittin da biyar.

AGADEZ

Yankin Agadez shi ne ya fi kowanne yanki girma a Nijar, wanda girmansa ya kai murabba'in kilo mita 634,209, watau kwatankwacin kashi 52 cikin dari na girman Nijar baki daya.

Yankin Agadez ya hada da hamadar Tenere da Bilma da kuma yankin Air mai cike da tsaunuka.

Mafi yawancin jama'ar yankin Abzinawa ne; akwai kuma Tubawa da Fulani da kuma Hausawa.

Babbar sana'ar jamaar yankin ta asali itace cinikin gishiri da dabino, sai dai a shekarun 1990, harkar bude ido ta zama wata babbar sana'ar yankin, hakanan karfen Uranium da ake samu a garin Arlit na samawa Nijar kashi 20 cikin dari na kudin shigar da take samu.

Ayyukan tawaye da fari da aka rika samu a baya-bayan nan sun durkusar da tattalin arzikin yankin Agadez.

Image caption Jamhuriyar Nijar dai na da fadin kasa sosai

DIFFA

Yankin Diffa yana bangaren kudu maso gabashin Nijar, kuma yana da girman murabba'in kilo mita 156,906.

Diffa na iyaka da yankin Agadez ta Arewaci da Zindar ta Yammaci da Najeriya ta kudanci sai kuma Chadi ta Gabashi.

Yankin Diffa ya kasance daya daga cikin yankunan da ba su da yawan jama'a, wanda kidayar shekara ta 2001, ta nuna yawan mutanen yankin ya kusa dubu dari hudu.

Jama'ar yankin Diffa sun hada da Kanuri da Tubawa Hausawa da Fulani da Larabawa.

Tattalin arzikin yankin Diffa ya ta'allaka ne kan kiwo da noman rani da kuma na damina. #

Abubuwan da aka fi nomawa a yankin sun hada da gero da masara da shinkafa da kayan lambu irin timatir da barkono.

Sai dai kuma duk da noman da ake yi a Diffa, yankin ya kasance mafi koma baya ta fuskar noma a Nijar saboda fari.

DOSSO

Yankin Dosso na da girman murabba'in kilo mita 31,002, kuma kidayar da aka yi a shekara ta 2001, ta nuna yawan jama'ar yankin ya kai 1,479,095.

An kasa yankin Dosso zuwa jihohi biyar da suka hada da Boboye da Dogondoutchi da Dosso da Gaya da kuma Loga.

Yankin Dosso na iyaka da jihar Sokoto da Kebbi na Nijeria ta bangaren Kudu maso Gabas da jihar Alibori ta kasar Benin ta Kudanci.

A cikin gida kuma yankin Dosso na iyaka da yankin Tahoua ta Arewa maso Gabas da kuma yankunan Tillabery da Yamai ta Yammaci. Babbar sana'ar yankin Dosso ita ce noma.

MARADI

Yankin Maradi na da girman murabba'in kilo mita 35,100, kuma yana iyaka da Arewacin Najeriya ta Kudanci da yankin Tahoua ta Yammaci, sai yankin Zinder ta Gabashi.

Kidayar shekara ta 2001 ta nuna yawan jama'ar yankin ya kai 2,235,748, wanda hakan ya nuna shi ne yanki mafi yawan jama'a wadanda yawancinsu Hausawa ne.

Akan yiwa yankin Maradi kirari da cibiyar ciyar da kasa, sabili da harkokin kasuwanci da noman da ake yi a yankin.

Yawancin abubuwan da ake nomawa a yankin domin amfani da su a cikin gida da fitarwa waje sun hada da gyada da hatsi da gujjiya, ko da yake a wasu wuraren akan noma taba da mangwaro da alkama da waken soya da ma auduga.

Duk da irin wannan kirarin da ake yiwa yankin Maradi, jama'ar yankin na yawan fama da yunwa ko Tamowa musamman a duk lokacin da aka samu karancin ruwan sama a kasar.

TAHOUA

Tahoua na daga cikin yankuna takwas da ake da su a Jamhuriyar Nijar kuma tana da girman murabba'in kilo mita 106,677.

Kidayar da aka gudanar a shekara ta 2001, ta nuna cewa yawan jama'ar yankin sun kai 1,972,729. Kuma yawancinsu Hauwasa da Adarawa da Abzinawa da Larabawa.

Babbar sana'ar wannan yanki ita ce noma da kiwo.

Yankin Tahoua na makwabtaka ta kudanci da jihar Sokoto ta Najeriya da Yankin Gao na kasar Mali ta Yammaci, da kuma yankin Kidal na kasar ta Mali ta Arewa maso Yammaci.

TILLABERI

A shekarar 1992 ne aka kirkiro yankin Tillaberi lokacin da aka raba yankin Niamey.

Yankin na da girman murabba'in kilo mita 89,623, kuma kidayar jama'a ta shekara ta 2001, ta nuna yawan jama'ar yankin ya kai 1'889,515.

Yawancin mazauna Tillaberi Zabarmawa ne wadanda sana'arsu noma da kasuwanci ne.

Tillabery shi ne yankin Nijar kadai dake makwabtaka da kasar Burkina Faso, inda yake iyaka da yankin Seno ta Yammaci da Yagha ta Kudu maso yamma da Komondjari da Tapoa.

Sai yankin Gao na kasar Mali da Alibori na kasar Benin.

ZINDER

Yankin Zinder ko Damagaram na da girman murabba'in kilo mita 145,430, kuma kidayar da aka yi a shekara ta 2001 ta nuna yawan jama'ar yankin sun kai 2,080,250.

Kabilun dake zaune a yankin Zinder sun hada da Hausawa da Kanuri da Fulani da Larabawa da Abzinawa. Har zuwa shekara ta 1926, birnin Zinder ne babban birnin Nijar.

Yawancin tattalin arzikin yankin Zinder ya dogara kan noma da kiwo da kuma kasuwanci.

Yankin Zinder na makwabtaka da wasu jihohin Najeriya kamar jihar Jigawa ta Kudu sai jihar Katsina ta Kudu maso Yamma.

A cikin gida kuma yankin Zinder na iyaka da Agadez ta Arewaci da Diffa ta Gabashi da Maradi ta Yammaci.

NIAMEY

Niamey shi ne babban birnin Jamhuriyar Nijar, wanda shi ne birni mafi girma a kasar, dake da girman murabba'in kilo mita 239.30.

Tun a karni na 18 ne aka kirkiro Niamey, sai dai a wancan lokacin ba'a dauke shi da wani muhimmanci ba har sai bayan da Faransa ta kafa cibiyarta a wajen a shekarun 1890.

A shekarar 1926 ya zamo babbar birnin kasar ta Nijar. Sannu a hankali yawan jama'ar yankin ya yi ta karuwa daga 3,000 a shekarar 1930 zuwa kimanin 30,000 a shekarar 1960.

Yawan jama'ar Niamey ya kai 250,000 a 1980, a shekara ta 2000 kuma 800,000.

Babban musabbabin karuwar jama'a a Niamey shi ne na yawan kaurar jama'a a lokutan fari.

A matsayinsa na babban birnin Jamhuriyar Nijar, akwai wuraren tarihi da suka hada da gidan tarihi na kasa da gidan zoo, akwai kuma cibiyoyin nuna al'adun gargajiya na Amurka da Faransa da Nijar.

Hakanan kuma akwai manyan kasuwanni bakwai a birnin.

Kashi 90 cikin dari na jama'ar Niamey Musulmai ne, anan ne kuma ake da hedkwatar mabiya darikar kirista ta Roman Katolika.