Likitoci na yin tiyatar ido kyauta a Katsina

Nigeria
Image caption Nigeria

A Nijeriya, Kungiyar wasu kwararrun likitoci daga kasar Pakistan sun kaddamar da wani shiri na tiyatar ido kyauta a sassa dabam-dabam na kasar.

A karkashin wannan shiri da yanzu haka ke gudana a Katsina, za a yi wa mutane kimanin 600 ne tiyatar idon ta yadda za su iya gani su kuma iya dogara da kansu.

Tarayyar Kungiyar likitoci Musulmi ce dai ta gayyato kwararrun likitocin wadanda ke yin wannan aiki tare da da hadin-gwiwar kungiyar Ecological Consultants ta Nijeriya.

Akwai dai kungiyoyi dabam-dabam a kasar ke gudanar da irin wannan aiki kyauta.