Majalisar dattawan Najeriya na neman a yi zabe a watan Janairu

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Image caption Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Rahotanni daga Najeriya sun ce, majalisar dattawan kasar ta amince da wani gyara, wanda ya tanadi a gudanar da babban zaben kasar a watan Janairun badi.

Gyaran ya bukaci a gudanar da zabe a cikin kwanaki 120 zuwa 150 kafin karshen wa'adin ikon shugaban kasa, a maimakon kwanaki 30 zuwa 60.

Wasu na ganin cewa za a sami raguwar yawan lokacin gudanar da yakin neman zabe, kuma hukumar zaben kasar mai zaman kanta, INEC, ba za ta sami isasshen lokacin shirya zabubukan ba, ganin cewa a kwanan nan ne ma ta sauya wasu shugabannin ta.