Nijar ta fara shirye-shiyen kidayar al'umma

Shugaban mulkin sojan jamhuriyar nijar,Saliou Djibo

Gwamnatin Nijar ta fara shirye-shiryen gudanar da kidayar al'umma, wacce za ta bada damar sanin adadin jama'ar kasar.

Hukumar kididdiga a fannin tattalin arziki da jin dadin rayuwar jama'a,wacce zata gudanar da aikin, ta ce tana bukatar sefa biliyan goma sha daya don gudanar da shi.

Ranar Talata ne hukumar kididdigar ta kira wani taro da ya hada da wakilan gwamnati, da masu ruwa da tsaki a kasar,inda ta sanar dasu a inda aka kwana dangane da shirye shiryen gudanar da kidayar.

Wannan shi ne karo na hudu Nijar na shirya kidayar al'umar kasar,bayan wadanda aka yi a shekarar alif dari tara da saba'in da bakwai, da alif dari tara da tamanin da takwas, da kuma shekarar 2001.