Human Rights Watch ta yi kiran a yi bincike a Rwanda

Shguaban Rwanda, Paul Kagame
Image caption Shguaban Rwanda

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta nemi gwamnatin Rwanda ta baiwa kwararru masu zaman kansu damar yin bincike kan gawar Andre Kagwa Rwisereka.

An dai hallaka Mr Andre Kagwa Rwisereka wanda kuma dan adawa ne a farkon watan nan.

Kungiyar tace akwai kura-kurai da dama a bayanan da mahukunta su ka bayar dangane da kisan nasa.

Yan sanda sun ce an kashe Mr. Rwisereke a wani sabani da ya shafi hada-hadar kudi.

To saidai 'yan kwanaki kadan gabanin a hallaka shi, dan siyasar ya shaidawa abokansa cewa ya na fuskantar barazanar kisa saboda adawar da ya ke da gwamnati.

Wakilin BBC ya ce kisan Mr. Rwisereka ya biyo bayan hare-haren da aka kaiwa wasu masu adawa da gwamnatin shugaba Paul Kagame ne.

Dama a watan jiya an harbi wani tsohon shugaban rundunar sojin Rwanda, janar Kayumba Namwasa a Afrika ta kudu.