Soyinka zai shiga siyasa

Fitaccen marubuci,farfesa Wole Soyinka
Image caption Farfesa Soyinka zai tsunduma cikin siyasar Najeriya

Fitaccen marubucin nan na Najeriya,farfesa Wole Soyinka ya ce zai tsunduma cikin harkokin siyasar kasar gadan gadan.

Wole Soyinka,wanda ya taba cin lambar yabo ta Nobel ya ce a watan satumba ne zai kafa wata Jam'iyyar siyasa don kawo sauyi a harkar siyasar kasar.

Shi dai Mr Soyinka wanda ba'a san shi da shiga harkar siyasa ba, ya fadi haka ne ranar Talata a birnin Lagos, wurin wani taro don tunawa da zagayowar ranar haihuwarsa shekaru saba'in da shida da suka gabata.

Masana na ganin cewa fadawar farfesa cikin harkokin siyasar kasar abin mamaki ne tunda dai ya sha sukan tsarin siyasar kasar.