Nijar da Burkina Faso na gaban Kotun Duniya

Taswirar Nijar
Image caption Kotun Duniya ta ce za ta gano inda ya kamata a shata iyaka tsakanin Nijar da Burkina Faso

Kasashen Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar sun bukaci Kotun Duniya da ke birnin Hague ta shiga tsakaninsu dangane da wata rigimar kan iyaka da ta ki ci ta ki cinyewa.

Dukkan kasashen biyu dai Faransa ce ta yi musu mulkin mallaka, kuma a bara ne suka amince su kai wannan batu gaban Kotun.

Kotun ta Duniya dai ta ce za ta gano inda ya kamata a shata iyaka tsakanin kasashen biyu a yankin da ke da nisan kilomita kusan dari uku da saba'in da biyar.

Kasashen biyu sun amince su tabbatar da zaman lafiya da tsaro a tsakaninsu kafin Kotun ta kammala duba bukatar tasu.