An zargi kotun duniya da nuna son kai

Shugaba Omar al-Bashir
Image caption Shugaba al-Bashir ya dade yana shan suka daga kasashen yamma

Kasar Chadi ta zargi kotun hukunta laifukan yaki ta duniya (wato ICC) da nuna son kai wajen hukunta kasashen Afrika, a wani yunkuri na kare matakin da ta dauka na kin kama shugaban Sudan.

Jakadan Chadi a Amurka ya shaidawa BBC cewa tsarin shari'a kan kasa yin tasiri idan dai babu adalci a ciki.

Ita dai kotun ta ICC ta zargi shugaba Bashir da aikata laifukan yaki da kisan kare dangi - zargin da ya musanta. Kasar Chadi ce ta farko daga cikin kasashen da suka sa hannu kan dokar ta ICC, da Mista Bashir ya ziyarta tun bayan da kotun ta ICC ta ba da sammacin kama shi a shekarar 2009.

Duka shari'o'i biyar din da ke gaban kotun dai sun fito ne daga nahiyar Africa, amma kotun ta ce kasashe ne ya kamata su mika mata bayanai sannan ita kuma ta bincika.

An dai kafata ne domin hukunta laifuffukan da suka shafi cin zarafin bil adama da kisan kare dangi. Amma babban mai gabatar da kara na kotun ya yi watsi da zargin, yana mai cewa a nahiyar aka aikata manyan laifuffuka, sannan kuma wadanda abin ya shafa ma 'yan nahiyar ne.

Kungiyar Tarayyar Afrika da ta Hadin kan Kasashen Larabawa, sun nuna adawa da matakin kotun na ba da sammaci kan rikicin yankin Dafur na Sudan.

Image caption Shugaba al-Bashir a wani gangamin siyasa

Bin doka da oda

Jakadan Chadi, Ahmat Mahamat Bachir, ya gayawa shirin BBC na World Today cewa : "Muna bin doka da oda, kuma ya kamata a hukunta duk wanda a ka samu da laifi, amma idan aka nuna sankai to ba za mu amince ba."

Ya ce akwai shugabannin kasashe da dama da ya kamata a dauki mataki a kansu kamar yadda a ka dauka a kan Mista Bashir, amma ya ki ya ambace su.

An dai zargi Mista Bashir ne da marawa Larabawa masu dauke da makamai baya domin kai hari kan bakaken fata fararen hula a yankin Dafur a shekara ta 2003.

Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa akalla mutane 30,000 suka rasa rayukansu, yayinda wasu miliyan biyu da doriya suka rasa matsugunansu.

Amma Sudan ta zargi kasashen yamma da ingiza abubuwan da ke faruwa a yankin. Shugaba Bashir dai na halartar taron kasashen yankin Sahel ne a kasar ta Chadi.

Mai magana da yawun kotun ta ICC ya ce akwai bukatar Chadi ta goyi bayan hukuncin alkalan kotun ta kama Shugaba Bashir.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International, ta nemi Chadi da ta kama mista Bashir, tana mai cewa wannan wata dama ce da shari'a za ta yi aikinta.

Image caption A farkon shekara mai zuwa ne za a kada kuri'ar neman raba yankin Kudu da Arewacin Sudan

Zabi ga shugaba Bashir

Wakilin BBC a yankin gabashin Afrika, Will Ross, ya ce zabi na gaba ga Mista Bashir, shi ne ko zai halarci taron Kungiyar Tarayyar Afrika da za a yi a Uganda.

Tarayyar Afrika ta zargi kotun ICC da muzgunawa kasashen Afrika, sannan ta nemi kasashen da kada su bada kai bori ya hau. Kamar Chadi - Uganda ma dai mamba ce ta kotun.

Dangantaka tsakanin Sudan da Uganda ta yi tsami, abin da yasa mai yiwuwa shugaba Bashir ya sauya tunani ya zarce gida, maimakon yin kasadar zuwa taron na Uganda.