Majalisar Najeriya ta amince da bukatar INEC

Shugaban Hukumar Zabe ta Najeriya, Farfesa Attahiru Jega
Image caption Majalisar Dattawan Najeriya ta aiwatar da gyare-gyaren da INEC ta ce in ba a aiwatar ba ba za ta iya gudanar da zabe a watan Janairu ba

Majalisar Dattawan Najeriya ta aiwatar da wadansu gyare-gyare wadanda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC a Turance) ta ce idan ba a aiwatar ba da wuya ta iya gudanar da babban zaben kasar a watan Janairun badi.

Daya daga cikin dokokin da aka yiwa garambawul ita ce dokar da ta wajabtawa hukumar kammala aikin rajistar masu kada kuri'a kwanaki dari da hamsin kafin ranar zabe, amma yanzu sabon fasalin dokar ya tanadi yin rajistar masu zaben ne kwanaki sittin kafin zabe.

Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya shaidawa BBC cewa Hukumar Zaben ta “rubuto mana a rubuce [ta] fadi koke-kokenta [tana] so mu gyara dokar yadda za su iya samun sasssauci”.

Wannan matakin dai babu shakka zai farantawa wasu kungiyoyin farar hula da dama ke cewa gudanar da zabe a watan Janairu ba shi da fa'ida don hukumar zaben ba za ta samu isasshen lokacin shirya zabe mai tsafta ba.

Mallam Awwal Rafsanjani na kungiyar CISLAC mai sa ido a kan harkar majalisun dokoki a Najeriyar yana ganin cewa gudanar da zaben a watan Janairu bai dace ba.

A cewarsa: “Babban dalilin da ya sa muke kira cewa lallai lallai a baiwa hukumar zabe cikakken lokaci don ta canja kundin rajistar masu zabe [shi ne] mun san cewa ba za a samu kashi goma cikin dari na kuri’un da za su iya tabbatar da zabe mai martaba a shekarar 2011 ba.... Meye amfanin yin zaben da ba rajista; ko kuma meye amfanin zaben da za a yi, jama’a ba za su samu damar sa hannu a kan abin da suke so ba?”.

Karin bayani