An samu Trafigura da laifin jibge guba

Wata da gubar sharar ta yi illa a Abidjan.
Image caption Jibge shara mai guba a Abidjan ta janyo

Wata kotu a kasar Holland ta sami babban kamfanin Trafigura da laifin kai shara mai guba a nahiyar Afirka daga Turai, ba bisa ka'ida ba.

An dai ci kamfanin na Trafigura tarar fiye da dala miliyan guda, saboda ya jibge sharar mai guba a birni mafi girma a kasar Cote d'Ivoire, watau Abidjan.

Dubban jama'a sun kwanta rashin lafiya, kuma cibiyoyin lafiya a birnin sun cika sun batse.

Kamfanin na Trafigura dai ya ce, bai ji dadin hukuncin ba, kuma zai yi nazari a kansa, da zummar daukaka kara.

A nata gefen, kungiyar Greenpeace mai fafutukar kare muhalli ta ce, hukuncin kotun, hannunka mai sanda ne ga masu jibge shara ba bisa ka'ida ba, cewa akwai ranar kin dillanci.