Ta da kayar baya ya ragu a Afghanistan

Janar David Petraeus
Image caption Sabon kwamandan sojojin Amurka a Afghanistan, Janar David Petraeus, na duba yiwuwar sassauta sharuddan

Wani sabon rahoto ya bayyana cewa iyakokin da aka shatawa sojojin kawance a Afghanistan da nufin takaita yawan fararen hular da ke jikkata ya rage yawan hare-haren tayar da kayar baya a kan rundunonin na kasashen waje.

Rahoton, wanda Cibiyar Binciken Tattalin Arziki ta Kasar Amurka ta gudanar, ya ce wannan mataki ya haifar da ingantuwar tsaro a kasar ta Afghanistan.

Rahoton dai ya yi nazari ne a kan mutuwar fararen hula dubu hudu a wadansu daga cikin yankunan Afghanistan, inda ya gano cewa a wuraren da sojojin kawancen suka hallaka mutane biyu, an samu karin tayar da kayar baya shida har na tsawon makwanni shida.

Dalili kuwa, inji rahoton, shi ne sau da yawa kisan fararen hula na tunzura mutanen kauyukan da abin ya shafa su shiga kungiyoyi masu tayar da kayar baya.

Janar Stanley McChrystal ne dai ya gitta sharuddan bude wuta ga sojojin Amurka a wani yunkuri na kwantar da hankulan mutanen Afghanistan.

Sai dai yayinda ake bukin karrama Janar McChrystal, wanda ya yi murabus bayan Shugaba Obama ya sauke shi daga kan mukaminsa, magajinsa, Janar David Petraeus, yana duba yiwuwar sassauta sharuddan.

Wasu sojoji sun yi korafin cewa takaita kai hari ta sama na kara tsananta hadarin da suke fuskanta yayin gudanar da ayyukansu.

To amma za a yi amfani da wannan rahoto don nuna cewa al'amarin ba haka yake ba.