Kampanin BP zai fara hakar mai a yankin ruwayen Libya

Tambarin kamfanin man BP
Image caption Tambarin kamfanin man BP

Kampanin man Birtaniya na BP ya tabbatar da cewar, zai fara aikin hakar mai a can cikin teku kusa da Libya, cikin makonni masu zuwa.

Sanarwar ta zo yayin da ake ci gaba da nuna damuwa da batun da ya shafi kare muhalli da matakan kare lafiyar da kampanin na BP ke dauka, bayan malalar man da aka samu a tekun Mexico.

Ana dai tambayoyi kan yadda kampanin ya samu kwangilar aikin man da kuma iskar gas daga Libya, a daidai lokacin da ake zarginsa da yin amfani da fada-ajinsa, wajen sawa a sako mutumin da aka samu da laifin kai harin bam na Lockerbie, Abdelbaset el Megrahi, tare da mai da shi Libya. BP dai ya musanta zargin.