Gordon Brown ya bukaci a habaka tattalin arzikin Afirka

Tsohon Praministan Birtaniya Gordon Brown
Image caption Tsohon Praministan Birtaniya Gordon Brown

An bukaci shugabannin kasashen Afirka da su samar da wata sabuwar hanya, ta tunkarar batun habakar tattalin arziki da kuma samun agaji a nahiyar.

A yayin da shugabanin Afirkan ke hallara a Uganda, domin taron kolin tarayyar Afrika, tsohon Praministan Birtaniya Gordon Brown, ya shaidawa wani taron share fagen taron kolin cewa, ya kamata a maida hankali wajen samar da ayyukan yi ga miliyoyin jama'a, a kuma yi amfani da agajin raya kasa wajen karfafa harkokin kasuwanci masu janyo bunkasar tattalin arziki, ba wai a maye gurabensu ba.

Mr Brown ya kuma ce, tattalin arzikin duniya zai amfana idan duniya ta maida hankalinta kan Afrika, wadda ya ce tana cike da albarkatu, da kuma mutane masu basira.

Wannan ne karon farko da Mr Brown ya bayyana a gaban wani taro, tun bayan faduwarsa zabe a watan Mayu.