Firayim minista ya ajiye shugabancin jam'iyya

Taswirar Ivory Coast
Image caption Ivory Coast ta dare gida biyu: arewaci na karkashin tsofaffin 'yan tawaye, kudanci na karkashin Shugaba Laurent Gbagbo

Firayim ministan Ivory Coast, Guillaume Soro, ya yi murabus daga kan mukaminsa na shugaban jam'iyyar nan ta tsofaffin 'yan tawaye, wato New Forces.

A wata sanarwa da ya fitar, Mista Soro ya ce ya dauki wannan mataki ne domin ya samu damar mayar da hankali ga shirya zaben shugaban kasar wanda aka rika jinkirta shi kowacce shekara tun shekarar 2005.

Ivory Coast dai ta dare gida biyu, inda Mista Soro da dakarunsa ke iko da arewacin kasar, yayin da gwamnati kuma ke iko da kudancin kasar, tun bayan yunkurin juyin mulkin da aka yiwa Shugaba Laurent Gbagbo a shekarar 2002.

Tun a shekarar 2007 ne kuma bangarorin biyu ke aiki kafada-da-kafada a wata gwamnatin hadin gwiwa.