Taron shugabannin kasashen Afirka a Uganda

Taron kungiyar kasashen Afirka AU
Image caption Shugabannin kasashen Afirka zasu gudanar da taro a kasar Uganda domin tattauna batutuwa da suka shafi yankin ciki harda batun rikicin kasar somalia

Shugabannin kasashen nahiyar Afirka za su gudanar da taron tarayyar Afirka a kasar Uganda, wanda ake sa ran batun rikicin kasar Somalia ne zai mamaye ajandar taron.

Taron na zuwa ne makonni biyu, bayanda wani harin bam yayi sanadiyyar rasuwar mutane fiye da 70 a Uganda, wadda ita ce daya daga cikin kasashen da suka fi yawan sojojin kiyaye zaman lafiyar tarayyar Afirka a kasar Somalia.

kungiyar 'yan bindiga ta Al Shabab tace ita ce keda alhakin fashewar bama baman, a saboda haka ba abin mamaki bane taron shugabannin kasashen afirkan zai maida hankali akan matakin da zai dauka saboda wannan rikicin Somaliyan.

Taron shugabannin kasashen Afirkan zai kuma tattauna batun lafiyar kananan yara da kuma mata