Anyi hasashen karin ruwan sama mai yau a China yau

Ambaliyar ruwa a kasar Sin
Image caption Cibiyar kula d ayanayi ta kasar Sin tayi hasashen saukar ruwa kamar da bakin kwarya a yau lahadi

Cibiyar kula da yanayi ta kasar China, ta yi hasashen cewa, ruwan sama kamar da bakin kwarya zai cigaba da sauka yau lahadi, yayinda mutane fiye da dubu dari suka bar gidajensu, domin kaucewa ambaliyar ruwan dake barazana ga yankuna da dama na kasar.

Rahotanni na nuna cewa adadin ruwanda aka ajiye a madatsun ruwa guda ukku dake kogin Yangtze, ya ragu da fiye da santimita 15.

Injiniyoyi ne ke bude madatsun ruwan, to amma su na kokarin hana ruwan fita da yawa, domin kaucewa ambaliyar ruwan wanda tuni ya malale yankunan dake kasa-kasa.

A lardin Gansu dake arewa maso yammacin kasar mutane 13 ne suka mutu sakamakon murgunowar kasa.

Firayim Ministan kasar Sin ya gargadi jami'ai dasu shiryawa ambaliyar ruwa mafi muni