FFR ta yi kiran a share nakiyoyi a Nijar

A jamhuriyar Nijar, tsohuwar kungiyar tawayen FFR ta Rhissa Ag Boula, tsohon minista a gwamnatin kasar, ta yi kira ga sauran tsoffin kungiyoyi tawaye da su bada hadin kai, wajen gudanar da aikin tono nakiyoyi a yankin arewacin kasar, inda suka kwashe shekaru ukku suna gwabza fada dakarun gwamnati.

Wani hadin gwiwa ne da ya hada gwamnatin Niger, da Hukumar raya karkara ta majalisar dinkin duniya, UNDP, da kungiyar kula da wadanda suka yi hatsari, watau HANDICAP INTERNATIONAL, shi ne ke aikin kwance nakiyoyin a yankin Agadez.

A karshen shekarar da ta wuce ne aka kulla yarjajeniyar kawo karshen yakin tsakanin gwamnati da 'yan tawayen.