Atisayen dakarun Amurka dana Koriya ta Kudu

Shugaba Barack Obama dana Koriya ta Kudu Lee Myungbak
Image caption Sojojin hadingwiwa na kasashen Amurka da Koriya ta Kudu na daf da fara wani gagarumin atisaye

Atisayen sojojin hadin gwiwa tsakanin Amurka da Korea ta Kudu na gab da farawa a gabar tekun Korea, duk da barazanar da Korea ta Arewa ta yi na yiwuwar daukar fansa.

Dakaru dubu takwas ne na sojojin Amurka da na Korea ta Kudu za su gudanar da wannan atisaye, da jiragen ruwa na yaki 20 da kuma jiragen sama na yaki 200

Korafin da kasar Koriya ta Arewa take yi dangane da wannan atisaye dai na karuwa amma ga kassahen amurka dana koriya ta kudu kuwa hakan shine ma dalilin dayasa suke gudanar da atisayen.

Rashin jituwar dake tsakani dai na janyo damuwa a yankin abinda yasa kasar China take rokon kasashen biyu dasu kwantar da hankulansu