An bude taron kolin Afrika a Uganda

Shugaba Museveni na Uganda
Image caption Shugaban Uganda, Yoweri Museveni, a taron kolin kasashen Afrika, a Uganda

Shugaban Uganda, Yoweri Museveni, yayi kira ga kasashen duniya da su hada kai domin murkushe masu gwagwarmayar Musulunci a Somaliya.

Yayi kiran ne yayin da aka soma taron kolin Tarayyar Afirka a Kampala, babban birnin Ugandar - 'yan makonni kuma bayan hare-haren da aka kai a birnin Kampalar, inda aka hallaka mutane fiye da saba'in.

Kungiyar al-Shabaab ta Somalia ce ta dauki alhakin kai hare-haren.

Uganda ce kasar da ta fi bada gudunmawar soja a rundunar Tarayyar Afirka da ke aikin kiyaye zaman lafiya a Somalia.