Yau kusoshin PDP na kudu ke taro.

'Yan siyasa a yankin kudu maso kudancin Nijeriya sun yi kira ga 'yan arewacin Nijeriya da su goya wa shugaba Goodluck Jonathan baya domin neman zama shugaban kasa a zaben da za a gudanar a badi.

Jiga-jigan 'yan siyasa da sarakunan gargajiya, da sauran masu fada aji a yankin suna gudanar da wannan taro ne a birnin Fatakwal domin nuna goyon baya ga Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ci gaba da mulki.

Cif Tony Anenih, wani tsohon minista, yana cikin na kan gaba wajen wannan kira na neman goyan baya ga shugaba Jonathan.

Taron ya sami halartar akasarin gwamnonin yankin 'yan jam'iyyar PDP.