Kungiyar Amnesty International ta ja hankalin kasar Girka

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International
Image caption Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ja hankalin kasar Girka akan kare hakkin 'yan cirani

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta bukaci kasar Girka da ta dakatar da yadda take daukar masu neman mafaka dake kasar tamkar masu laifi da kuma kulle su a kurkuku.

A cikin wani sabon rahoto da ta wallafa kungiyar ta nuna damuwarta matuka game da yadda yara kanana suke karewa a cibiyoyin da ake tsare masu laifi a kasar Girkan.

Nicola Duckworth shine daraktan shirye shirye na kungiyar a turai da kuma tsakiyar nahiyar asiya, ya kuma bayyana cewa masu neman mafakar ba masu laifi bane, sai dai duk da haka hukumomin kasar Girkan basa basu hakkinsu karkashin dokokin kassahen duniya

A halinda ake ciki inji shi ana tsare 'yan ciranin dake shiga kasar ba tare da yin la'akari da ko hakan shine daidai ba