Jam'iyyar PDP a jahar Kaduna ta amince da takarar Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Image caption Jamiyyar PDP a jahar Kaduna tace ta amince shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya tsaya takarar shugabankasa a shekarar 2011

Jam'iyyar PDP tare da gwamnatin jahar Kaduna sun amince da ture batun nan na karba- karba, batun dake haifar da kace nace tsakankanin 'yan arewacin kasar.

Jahar dai a yanzu tace ta dau matsayar amincewa shugaban kasar Goodluck Jonathan ya tsaya takara, haka kuma gwamnan jahar Patrick Ibrahim Yakowa shima ya yi takarar gwamnan jahar a shekarar ta 2011.

Wannan matsaya ta jahar wacce aka dauka a wani taron masu ruwa da tsaki na jahar Kadunan, bata yi daidai da tsarin karba-karba na jam'iyyar PDP a kasar da kuma jahar ba.

Sai dai wasu 'ya'yan jam'iyyar ta PDP a jahar sunce ba za su amince da wannan matsaya ba

Uwar jam'iyyar PDP dai bata fidda matsayinta ba dangane da wannan batu ya zuwa yanzu