Kotu a Cambodia ta yankewa Kaing Guek Eav hukunci

Kotu ta yankewa Kaing Guek Eav hukuncin daurin shekaru 35
Image caption Wata kotu a Cambodia dake samun goyan bayan kasar Amurka ta sami Kaing Guek Eav da aikata laifukan yaki

Wata kotu dake samun goyon bayan Amurka a kasar Cambodia ta samu Kaing Guek Eav wanda aka fi sani da Comrade Duch, tsohon shugaban gidan yarin Khmer Rouge, da aikata laifukan yaki.

Kotun ta kuma yanke masa hukuncin shekaru talatin da biyar a gidan kaso.

A zamanin mulkin Khmer Rouge a kasar Cambodia cikin shekarun 1970, Comrade Duch ya jagorancin gidan yarin Tuol Sleng, inda ake azabtarwa tare da hallaka wadanda ke adawa da gwamnatin kasar.

Wannan ne karon farko da aka yankewa wani babban jami'in gwamnatin Khmer Rouge hukunci, wacce tayi sanadiyyar ajalin kimanin mutane miliyan biyu.

An dai nuna zaman kotun kai tsaye a gidan talabijin kuma mutane da dama sun bayyana gamsuwarsu game da hukuncin