An wallafa sirrin dakarun Amurka a Afghanistan

Dakarun Amurka a Afghanistan
Image caption Wasu manyan jaridun duniya guda uku sun wallafa sirrin dakarun Amurka a Afghanistan

Wasu manyan jaridun duniya guda uku sun wallafa wasu rahotanni da suka jibanci wasu abubuwa da sojojin Amurka suka aikata a yakin Afghanistan wanda kuma ba'a taba ruwaitowa ba.

Rahotannin wanda jaridun Guardian da NewYork Times da ma jaridar Der Spiegal ta jamus suka wallafa, sun bayyana irin rawar da sojojin Amurkan suka taka a cikin shekaru shida a kasar Afghanistan.

Kodayake ba wasu sabbin abubuwa bane suka fito, sai dai Jaridun sun yi tsokaci ne akan irin wahalhalun yakin da kuma mace macen fararen hula.

Fadar White house dai ta yi Allawadai da labaran da jaridun suka wallafa tana mai cewar abubuwa ne da suka faru tsakanin shekarun 2004 zuwa 2009.