Kungiyar EU ta mayar da tallafinta ga Nijar

Rahotanni daga birnin Brussels Hedikwatar kungiyarr tarayyar Turai sun ce kasashen kungiyar za su mayar da tallafin kudi ga kasar ta Niger .

Amma kuma kungiyar ta ce lallai ne gwamnatin Majalisar Mulkin soja ta kasar ta mika mulki ga zabbabiyar gwamnati a watan Maris na badi.

Tarayyar Turan ta dakatar da tallafi ne na tsabar kudi Milyan 458 na kudin tarayya na Euro sakamakon canza kundin tsarin mulki da tsohuwar gwamnati ta yi domin zarcewar Malam Mamadou Tandja a kan mulki bara.