An nemi kotun ECOWAS ta sa a sako Tanja

A jamhuriyar Nijar lauyan tsohon shugaban kasar Malam Mammadou Tandja, Barrister Souley Oumarou, ya shigar da kara a gaban kotun kawancen tattallin arzikin kasashen Afrika ta YAMMA , ECOWAS/CEDEAO.

A karar ya nemi kotun ta sa Majalisar Mulkin Sojan Nijar, CSRD , ta sako Malam Mammadou Tandja, tare da ba shi damar tafiya neman magani, a duk kasar da yake so.

Tun bayan juyin mulkin da soji sukayi a watan Fabrairun bana ne suke tsare da shugaba Tandja.