Ci gaba da rashin tasirin shafukan sada zumunta

Shafin sada zumunci na Facebook ya bayyana cewa a yanzu haka mutane sama da miliyan dari biyar ne ke amfani da shafin wanda aka kaddamar shekaru shida da suka gabata.

A yanzu haka dai shafin na Facebook ya fi kowani shafi a shafukan sada zumunta na Intanet.

Duk da cewar an samu ci gaba a wasu shafukan sada zumunci, shafuka kamar su, MySpace da Flickr da kuma Bebo sun koma kasa ne a 'yan shekarun nan, kamar yadda kamfanin Nielsen ya nuna.

Abun mamaki a nan shi ne yadda aka samu banbanci tsakanin kasashen duniya, game da adadin mutanen da ke amfani da shafin na facebook da kuma lokacin da su ke amfani da shi.