Kusoshin PDP a yankin Neja Delta sunce sai Jonathan

Gwamnonin Jam'iyar PDP da ke Kudu Maso Kudancin Najeriya, sun amince su goya wa Shugaba Goodluck JonathanKasar baya, a zabe shekara ta 2011.

A taron da suka yi a birnin Fatakwal, na Jihar Ribas, Gwamnonin wadanda da suka hada da na Ribas, da Cross Rivers, da Akwa Ibom, da Bayelsa, da kuma Delta.

'Yan siyasar yankin kudu maso kudancin Nijeriyar sun kuma yi kira ga 'yan arewacin Nijeriya da su goya wa shugaba Goodluck Jonathan baya domin neman zama shugaban kasa a zaben da za a gudanar a badi.

Jiga-jigan 'yan siyasa da sarakunan gargajiya, da sauran masu fada aji a yankin ne suka halarci wannan taro.

Cif Tony Anenih, wani tsohon minista, na kan gaba wajen wannan kira na neman goyan baya ga shugaba Jonathan.