An wallafa bayanan sirrin yakin Afghanistan

Sojojin Amurka
Image caption Sojojin Amurka na sinturi a yankin Helmand na Afghanistan

Wani shafin Intanet mai suna Wikileaks ya buga wasu bayanai na sirri kan yakin Afghanistan. Buga irin wadannan bayanai dai a wannan shafi ba wani sabon abu bane.

A baya ma shafin ya sha buga bayanai wadanda suka ja hankalin kafafen yada labarai, musamman ma hotunan da shafin ya buga a baya inda aka nuna wasu hotunan bidiyo lokacin da wasu Amurkawa suke kashe fararen hula a Iraq.

A yanzu shafin yace yana da irin wannan bayanai sama da miliyan daya.

Tuni dai wasu manyan jaridun duniya guda uku suka wallafa bayanan, wadanda suka jibanci wasu abubuwa da sojojin Amurka suka aikata a yakin Afghanistan wanda kuma ba'a taba ruwaitowa ba.

Rahotannin wanda jaridun Guardian da NewYork Times da ma jaridar Der Spiegal ta jamus suka wallafa, sun bayyana irin rawar da sojojin Amurkan suka taka a cikin shekaru shida a kasar ta Afghanistan.

Jaridun sun yi tsokaci ne akan irin wahalhalun yakin da kuma mace macen fararen hula.

Musantawa

Fadar White House dai ta yi Allah wadai da labaran da jaridun suka wallafa tana mai cewar abubuwa ne da suka faru tsakanin shekarun 2004 zuwa 2009.

Amurka ta ce fitar bayanan ka iya jefa rayukan sojojin kawance da kuma na Afghanistan cikin hadari.

Image caption Fadar White House ta yi watsi da bayanan da aka wallafa

Itama gwamnatin Pakistan ta yi watsi da bayanan, bayan da suka zargeta da laifin hada kai da masu tayar da kayar baya na kungiyar Taliban.

Ofishin shugaban kasa ya bayyana cewa bayanan basu da makama, don haka bai kamata a amince da su ba.

Tasiri

Wakilin BBC na fannin tsaro Nick Childs, yace Irin adadin bayanan da suka fito da kuma lokacin fitowar ta su, ba karamin abin kunya bane ga gwamnatin shugaba Obama.

Baki daya babu wani bakon abu a bayanan da suka fito - ciki har da zargin dangantaka tsakanin jami'an leken asiri na Pakistan da masu tada kayar baya na Afghanistan. Sai dai zai yi wuya a iya gano ainahin tasirin da hakan ka iya yi.

Sai dai sun bayyana yadda jami'an Amurka suke rikon sakainar kashi da zargin dangantakar da ke tsakanin Pakistan da kungiyar Taliban.

Kuma hakan ya karfafa damar da ake da ita ta sukar jami'an na Amurka.

Image caption An dade ana zargin sojojin Amurka da laifin cin zarafin bil'adama

Bayanan sun zo ne a lokacin da Amurka da kawayenta ke kokarin neman goyon bayan jama'a kan matakan da ake dauka a Afghanistan, sai dai akwai damuwa da shakku a Washington da kuma sauran kasashe. Haka bayanan sun zo ne a lokacin da gwamnatin shugaba Obama ke kokarin maida hankali kan inganta dangantaka tsakanin Pakistan da Afghanistan.

Amma jami'ai a Amurka sun nace cewa babu daya daga cikin bayanan da ke tabbatar da ainahin halin da ake ciki a Afghanistan - ballantana ma tasirin dabarun shugaba Obama.

Abin jira a gani shi ne yadda wadannan bayanai za su yi tasiri kan alakar Amurka da Pakistan dama gwamnatin Afghanistan, kai harma da sauran kawayen Amurka.

Tare da sanya alamun tambaya kan yadda wadannan bayanai masu mahimmanci suka sulale ta irin wannan hanya.