Mutane fiye da ashirin sun hallaka a Afghanistan

Image caption Afghanistan

Mutane ashirin sun hallaka a Afghanistan

Hukomomin kasar Afghanistan sun ce akalla mutane ashirin da biyar ne suka rasu, kuma fiye da ashirin suka samu raunuka sanadiyyar fashewar bam a wata motar fasinja, a kudu maso yammacin kasar.

Gwamnan lardin Nimroz, inda bam din ya fashe, ya ce lamarin ya auku ne kan babbar hanyar data hada garin Nimroz da kabul babban birnin kasar.

Ya ce an kai wadanda suka jikkata asibiti, kuma mafi yawansu na cikin mawuyancin hali.