Pirayim Minista Cameron ya bukaci a shigar da Turkiya cikin turai

Pirayim Ministan Birtaniya, David Cameron, yayi wani kira da babbar murya na ganin an kyale Turkiyya ta shiga cikin kungiyar tarayyar turai.

A wani jawabi da yayi a Ankara, Mr Cameron, ya bayyana cewar shigar da Turkiyya cikin tarayyar turai zai kara karfafa wannan kungiya.

Mr Cameron ya ce sam ba daidai ba ne a ce Turkiyya zata iya zama 'yar gaadin Kofa, amma idan ruwa ya sauko ba zata a barta ta shiga ta fake a ciki ba. Ya ce,kawancen da na ke sa hannu a kai a yau tare da Pirayim Minista Erdogan ya zayyana irin burin da muke da shi na samar da wani kawance irin na zamani tsakanin Birtaniya da Turkiyya.

Ginshiki ga wannan kawance kuma shi ne Turkiyya ta cancanta a dama da ita cikin harkokin siyasar turai.