Hukumar zaben Nijar na kan hanyar sauke nauyin dake kanta

Shugaban hukumar zabe ta kasa a Jamhuriyar Nijar, mai shari'a Abdurahamane Ghousmane ya ce, tarayyar Turai ta baiwa hukumar albishir din kudi da yawansu ya kai Biliyan goma na CFA .

Hukumar dai na bukatar biliyan ashirin da tara ne domin gudanar da zabuka shidda a kasar .

Bugu da kari , hukumar zaben ta samu gudumawar wasu motocin aiki goma da na'urori masu kwakwalwa domin tafiyar da aikin zaben daga hukumar raya kasashe masu tasowa ta duniya UNDP/PNUD .

A wata hira da da manema labarai a birnin Yamai, shugaban hukumar zaben ta Niger ya ce kawo yanzu , hukumar zaben na kan jaddawalin kammalla zabbuka tare da rantsarda shugaban kasa a ranar sha daya ga watan Maris mai zuwa.