Wani jirgin sama ya fadi a Pakistan

Hadarin jirgin sama a Pakistan
Image caption Jami'an aikin ceto a Pakistan

Hadarin jirgin sama a Pakistan

Mahukuntan kasar Pakistan sun ce wani jirgin saman fasinja dauke da mutane fiye da dari daya da hamsin, ya fadi kuma ya kama da wuta a tsaunukan Margalla da ke kusa da Islamabad babban birnin kasar.

Jirgin saman mallakar kamfanin Air Blue ne, wanda ke jigillar fasinja a cikin gida, da kuma yankin Gulf da kuma Burtaniya.

Ma'aikatan ceto na kokarin isa wurin hastarin, sai dai rahtotanni sun ce wurin na da wuyar zuwa, ga shi kuma ana tafka ruwan sama.