Kwalara na yaduwa a Kamaru

Annobar cutar kwalara na ci gaba da yaduwa a yankin arewacin Kamaru.

A yanzu haka mutane 85 ne suka rasa rayukansu bayan bullar annobar a watan Yuni.

Haka kuma ana kiyasin cewar mutane fiye da dubu daya da dari daya ne suka kamu da cutar.

Jami'an ma'aikatar kiwon lafiya dai sun bayyana cewa duk da kokarin da gwamnati take yi tare da abokan huldarta akwai sauran aiki wajen shawo kan annobar.