Sace-sacen jama'a na janyo hallakar 'yan sanda a Najeriya

'Yan sandan Najeriya
Image caption 'Yan sandan Najeriya

A Najeriya rahotanni na nuna cewar kimanin jami'an 'yan sanda 27 ne suka rasa rayukansu, a fafutukar yaki da masu sace mutane bisa neman kudaden fansa a jihar Abiya.

A safiyar yau ma sai da rundunar 'yan sandan jihar ta ce ta cafke mutane 4 a garin Umuahiya, wadanda ake zargin sun yi barazanar kashe wasu mutane, muddin ba a biya wasu kudaden da suka nemi a sanya masu a asusun banki ba.

Wannan dai kari ne bisa adadin mutanen da rundunar 'yan sandan ta ce ta kama, bisa zargin aikata miyagun laifuffuka daban-daban a jihar.