Mutane 154 sun rasu a hadarin jirgin sama

Ma'ikatan ceto

Wani Jirgin sama dauke da mutane fiye da dari da hamsin ya fadi a kusa da Islamabad babban birnin kasar Pakistan.

Babu wanda ya tsira da ransa daga cikin hatsarin.

Masu aikin ceto sun gano gawawwaki daga cikin tarkacen jirgin, samfurin A-321 da ke ci da wuta.

Wadanda suka ga abun da ya faru, sun ce jirgin ya fada kan wani tsauni ne, a cikin tsananin hazo, inda nan take ya kama da wuta.

jirgin samar mallakar wani kamfanin zirga zirgar jiragen sama na Pakistan, Air Blue, ya fadi ne mintina kadan gabanin lokacin da aka shirya zai sauka a Islamabad.

Masu bincike suna gudanar da nazari akan faifan daukar bayanai na jirgin domin samun wata shaida akan dalilin da ya sa jirgin ya fadi.

A can wurin dake da tsaunuka wanda ke kallon babban birnin Pakistan, masu aikin ceto sun dukufa sa'o'i da dama suna aiki.

Jirgin dai wanda ya tarwatse yayi dai dai a wurin, na nisan 'yan mintuna kadan daga filin tashin jirgin saman garin.

Image caption Taswiran inda hadarin ya auku

Sai dai a cikin yanayi marar kyawu, da kuma ruwan da ake zabgawa a lokacin, sai jirgin ya fada dajin dake kan tsaunukan Margalla.

Wani wanda ya ganewa idanuwansa yanda abin ya faru, mai suna Samad Hassan Sharif ya bayyana cewa dama can yaji matukar fargaba kafin hadarin ya afku:

"A lokacin dana hango jirgin na ga cewa yayi kasa kasa, kimanin nisan mitoci dari da hamsin daga kasa, kuma da yake an dade ba'a ga jirgi a yankin ba, naji tsoro domin dai ya kaucewa hanyar da zai sauka, wato hanyar da jiragen kan bi".

Jita jita da fari wadda ke bayyana cewa akwai wadanda suka rayu dai ta kau.

Duka wadanda ke cikin jirgin dai sun rasu.

Karfin buguwar da jirgin yayi da tsaunukan, zai sanya da wahala 'yan uwan wadanda ke ciki su iya gane gawar 'yan uwan nasu.

Sai dai kuma har ila yau akwai korafi game da martanin da kamfanin jirgin wato Air Blue ya dauka.